✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kaduna ta ba ‘yan kasuwar Barci wa’adin kwanaki 3 su tashi

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da bayar da wa’adin kwanaki uku ga masu duk shaguna a kasuwar barci a jihar da su tattara su bar…

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da bayar da wa’adin kwanaki uku ga masu duk shaguna a kasuwar barci a jihar da su tattara su bar kasuwar .

‘Yan kasuwar sun tarar da sanarwar ne a safiyar ranar Asabar a shagunansu, inda sanarwar ke cewa gwamnatin ta ba kowa kwanaki uku kowa ya bar kasuwar.

Idan ba a manta ba kwanakin baya ne ake rade-radin cewa gwamnatin jihar za ta rushe kasuwar domin sauya mata fasali zuwa tsarin kasuwa ta zamani.

‘Yan kasuwar da dama sun koka dangane da wannan mataki na gwamnatin jihar, inda wasu ke cewa an basu wa’adi a kurarren lokaci.