✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Jihar Kaduna za ta koya wa matasa 6,000 sana’o’i

Gwamnatin Jihar Kaduna za ta fara shirin samar da matasa aikin yin da fara shirin koyar da matasa dubu shida (6,000) maza da mata sana’o’in…

 Gwamna Ramalan Mukhtar Yero na Jihar KadunaGwamnatin Jihar Kaduna za ta fara shirin samar da matasa aikin yin da fara shirin koyar da matasa dubu shida (6,000) maza da mata sana’o’in hannu, wanda akalla mutane 250 zuwa 300 daga kowace karamar hukuma za su amfana daga wannan shirin.
Shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, Alhaji Yahaya Aminu ne ya bayyana haka a wani taron yaye wasu dalibai 86, maza da mata da suka koyi sana’o’in hannu a karkashin kungiyar Raya Al’umma da Dogaro da Kai ta Khalifa Mahmoud da ke garin Kaduna a makon da ya gabata.
“Za a fara wannan shirin ne a satin farko na wannan wata na Agusta, kuma daga cikin kowace karamar hukuma, mun ware wani wuri na musamman wanda akalla mata dari za su rika amfana da shi a matsayin sashensu, kana suna gama koyon sana’o’in da za su yi na wata uku zuwa shida, za a ba kowa daga cikinsu jari.” Inji shi.
Ya kara da cewa gwamnati na da kyakkyawar manufa na ganin cewa ta karfafa wa duk wata kungiya irin waanan da ke da kokarin kawo ci gaba a cikin al’umma, musamman a irin wannan lokaci da muke ciki yanzu.
Shugabar kungiyar, Hajiya Maryam Yahaya Sani (Ameera), ta bayyana cewa kungiyar tasu, an kafa ta ne a shekarar 2010 don wayar da kan al’umma game da abin da ya shafi kiwon lafiya, da koyar da sana’o’i, musamman ga matasa maza da mata marayu da matan da mazajensu suka mutu.
Ta kara da cewa akalla matasa maza da mata dari ne suka amfana daga kungiya tun lokacin da aka kafa ta, kuma matasan da aka yaye yanzu 36 ne, sai mata 50, wadanda suka shafe watanni uku zuwa shida suna koyon sana’o’in iri daban-daban.
“Sana’o’in da matasan suka koya sun hada da fenti da rinin sutura da yin azara na zamani da hada turaren kanshi da hada sabulu da hada madarar Turawa da hada hodar koko da dai sauran wasu sana’o’in hannu, kuma duk wadanda suka koyi sana’o’in na nan na dogaro da kansu.” Inji ta.
A karshe Hajiya Maryam Ameera ta yi kira ga gwamnatin jihar da sauran kungiyoyi masu ba da tallafi su agaza ma kungiyarta da duk abin da ya dace domin ta samu damar tafiyar da ita yadda ya kamata.