Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya janye dokar kulle da ya sa da nufin dakile yaduwar cutar coronavirus a jihar har sai yadda hali ya yi.
Lalong ya sanar da haka ne a jawabinsa ga al’ummar jihar ta gidajen radiyo da talbijin, kan halin da ake ciki dangane da cutar ta coronavirus, a yammacin Alhamis.
Dokar kullen da Gwamnatin Jihar ta Filato ta sanya a da, tana aiki ne a ranakun Litinin zuwa Laraba, kafin a janye ta.
Gwamnan ya ce an janye dokar ne sakamakon fito da ka’idojin sassauta matakan kare yaduwar cutar da kwamitin da shugaban kasa ya kafa ya fitar, tare da kira ga jihohi da su kula da matakai a jihohinsu.
- COVID-19: Gwamnatin Filato ta sassauta dokar hana fita
- Ba mu janye dokar kulle kwata-kwata ba – Gwamnatin Kano
- An bude bankuna, an sassauta dokar kullen COVID-19
Ya ce don haka gwamnatin ta tattauna da masu ruwa da tsaki, sannan ta shirya taron kara wa juna sani kan yaki da cutar inda aka tattauna tare da bayar da shawarwarin yaki da cutar a jihar Filato.
Don haka gwamnatin jihar ta janye dokar har sai yadda hali yayi.
Gwamna Lalong ya ce a tsawon lokacin da aka dauka ana bin matakan kariya daga cutar a jihar, an yi wa mutum 2,032 gwaji cutar.
Daga cikinsu mutum 130 na dauke da cutar, an sallami 99 da suka warke, mutum 3 kuma suka rasu.
Ya zuwa yanzu kuma akwai mutum 26, da suke kwance ana yi musu jinya.