✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Filato ta fara tattaunawa da ‘yan Keke Napep

Gwamnatin Jihar Filato ta fara tattataunawa da masu sana’ar tuka Keke Napep, bayan dakatar da ayyukansu da gwamnatin jihar ta yi sakamakon zanga-zangar da suka…

Gwamnatin Jihar Filato ta fara tattataunawa da masu sana’ar tuka Keke Napep, bayan dakatar da ayyukansu da gwamnatin jihar ta yi sakamakon zanga-zangar da suka yi a ranar litinin din da ta gabata a garin Jos da kewaye wadda ya yi sanadin tsayawar harkokin yau da kullum tare da lalata motoci da ginin ofishin hukumar kiyaye hadaru ta kasa a garin na Jos.

Su dai masu tuka Keke Napep din sun gudanar da zanga-zangar ne don nuna rashin amincewarsu da shirin da ma’aikatar ayyuka da sufuri ta jihar ta fito da shi na basu horo tare da lasisin tuka Keke Napep da kowannensu zai kashe kudi naira dubu 5 da dari 800.

Masu zanga-zangar sun bi manyan hanyoyin cikin garin Jos,  har zuwa  gidan Gwamnatin Jihar, inda suka lalala motoci da dama tare da lalata ofishin hukumar kiyaye hadura ta kasa da ke Ring Road a garin Jos. Ganin haka ne ya sanya gwamnatin Jihar  ta dakatar da ayyukan masu Keke Napep din har sai yadda hali ya yi, a garin na Jos da kewaye.

Amma a ranar talatar da ta gabata gwamnatin jihar ta fara tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki kan wannan sana’a ta Keke Napep, don nemo hanyoyin  warware wannan matsala.

Da yake zantawa da jaridar Aminiya, shugaban kungiyar masu tuka Keke Napep reshen karamar hukumar Jos ta Arewa dahiru Hassan ya bayyana cewa, mun fara zama da gwamnatin jihar Filato don warware wannan matsala.

Ya ce a wannan zama gwamnatin ta bamu aikin mu je mu rubuto sunayen tashoshinmu da sunayen ‘yan kungiyarmu da lambobin wayarsu da lambobin Keke Napep din da suke tukawa.

Ya ce wasu tsuraru ne suka shiga wannan zanga zanga. Ya ce tun da farko da wadannan tsuraru sun yi aiki da dokokin wannan kungiya, wanda bai yarda da irin wannan zanga zanga ba, da  bata garin da  suka shiga wannan zanga zanga suka aikata wannan aika aika basu sami dama.  

Ya bada tabbacin cewa in Allah ya yarda nan bada dadewa ba za a janye wannan dakatarwa da aka yi masu. 

Ya baiwa al’umma hakuri kan mawuyacin  halin da suka shiga sakamakon dakatar da aikin ‘yan Keke Napep a garin na Jos da kewaye.  

Hakanan kuma, Malam dahiru Hassan ya bayyana cewa suna da matasa sama da dubu 30, da suke sana’ar tuka Keke Napep a Jihar Filato. 

Ya ce suna da Keke Napep sama da dubu 15 da matasa sama da dubu 30 da suke tukawa don ciyar da kansu da iyalansu.

Ya ce cikin wadannan matasa da suke wannan sana’a har akwai wadanda suka gama karatun jami’a, da sauran manyan makarantu.