✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Edo ta kara wa fursunonin da suka tsere wa’adin kawo kansu

Zaman lafiya na kara samuwa a jihar kuma muna godiya ga mutanen jihar da suke bin umurnin Gwamnati

Gwamnatin Jihar Edo ta kara wa fursunonin da suka tsere daga kurkuku a Benin da kuma Oko mako daya su kawo kansu.

Tun da fari dai Gwamna Godwin Obaseki ya ba fursunonin su 1,993 da ’yan daba suka bude a lokacin zanga-zangar #EndSARS a ranar Litinin kwanaki uku su dawo.

Mai ba gwamnan shawara kan harkokin watsa labarai, Crusoe Osagie ya ce, an kara wa’adin kwanakin ne bayan zama da Obaseki ya yi da shugabannin tsaro a Gidan Gwamnatin jihar a ranar Juma’a.

Ya ce, karin wa’adin na da alaka da ci gaba da dawowa da fursunoni suke yi gidajen yarin kamar yadda aka bukata.

Osagie ya ce, “Gwamna ya rage lokacin dokar hana fita da aka saka ta karfe 4 na yamma zuwa 6 na safe, ta koma 6 na yamma zuwa 6 na safe daga ranar Asabar, 24 ga watan Oktoba 2020.

“Zaman lafiya na kara samuwa a jihar kuma muna godiya ga mutanen jihar da suke bin umurnin Gwamnati.”

Ya kuma tabbatar wa mutane cewar gwamnati da taimakon jami’an tsaro a tsaye suke domin tabbatar da an samar da tsaro ga rayuka da kuma dukiyoyin al’umma.

Wadanda suka halarci taron sun hada da Mataimakin Gwamnan Jihar, Philip Shaibu da Sakataren Gwamnati Jihar, Osarodion Ogie; da Kwamishinan Shari’a Farfesa Yinka Omorogbe.

Sauran sun hada da shugabannin ’yan sanda; sojin kasa da na sama; gidan yari; tsaron cikin gida; da kuma Sibil Difens, dai sauransu.