✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Benuwai ta saki shanu 187 da aka rike

Gwamnatin jihar Benuwai ta sake sakin shanu 187 ga masu su, wanda suke hannun jami’an tsaro na dabbobi da ke biranan Makurdi babban birnin jihar.…

Gwamnatin jihar Benuwai ta sake sakin shanu 187 ga masu su, wanda suke hannun jami’an tsaro na dabbobi da ke biranan Makurdi babban birnin jihar.

Majiyarmu ta gano cewa, wannan shi ne karo na biyu da ake tsare dabbobin da suke shiga wurin da aka kafa doka a biranan jihar, a cikin mako guda an tsare shanu 105 inda kwanaki kadan aka baiwa wadanda suka mallake su.

Kwamishinan noma na jihar Benuwai Hyacinth Nyakuma ne sanar da hakan a Makurdi lokacin da yake mika dabbobin ga wadanda suka malleke su.