Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya dakatar da Sarkin Misau, Alhaji Ahmad Suleiman, a kan wani rikicin manoma da makiyaya da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum tara a masarautarsa.
Mummunan tashin hankalin dai, wanda ya kuma haddasa jikkatar mutane da dama, ya barke ne a garin Hardawa na karamar hukumar Misau kwana biyar da suka gabata.
Bangarorin biyu sun yi fito-na-fito ne a kan mallakar wani dajin gwamnati inda makiyaya suka dade suna kiwo, amma karamar hukumar Misau ta yi kokarin mayar da shi gonaki, lamarin da ya fusata makiyayan, ya kuma kai ga rikicin.
Hakimin Chiromah da Dagacin Zadawa na cikin ayarin masu sarautar da aka dakatar.
Saboda wannan rikicin ne dai Gwamna Bala Mohammed ya dakatar da shugaban riko na karamar hukumar ta Misau, Yaro Gwaram, ranar Laraba.
A daidai lokacin ne kuma ya dakatar da mataimakin shugaban karamar hukumar, Baidu Kafin-Misau, da sakatarenta, Sarki Usman Abdu.