✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Bauchi ta dage dakatarwar da ta yi wa Sarkin Misau

Sarkin Misau, Alhaji Ahmed Suleiman, ya dawo kan karagar mulkinsa bayan Gwamnatin Jihar Bauchi ta dage dakatarwar da ta yi masa. Babban Sakataren Gwamnatin Jihar,…

Sarkin Misau, Alhaji Ahmed Suleiman, ya dawo kan karagar mulkinsa bayan Gwamnatin Jihar Bauchi ta dage dakatarwar da ta yi masa.

Babban Sakataren Gwamnatin Jihar, Sabi’u Mohammed Baba, da Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati, Ladan Salihu ne suka damka wa basaraken wasikar dage dakatarwar, ranar Litinin, a fadarsa da ke Misau.

Idan ba a manta ba, an dakatar da  Mai Martaba Alhaji Ahmed Suleiman ne watanni hudu da suka da shude saboda rikicin kabilanci da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 11 a yankinsa.

Kwamitin da aka nada ya binciki musabbabin rikicin ya same shi da laifin sakaci da aiki wanda ake zargi yana daga cikin abubuwan da suka rura wutar rikicin.

A bayanin da Sarkin ya yi bayan karbar wasikar dawo da shi, ya jaddada mubaya’arsa ga gwamnatin jihar, ya kuma ce ba zai yi kasa a gwiwa ba na ganin al’ummarsa ta ci gaba da zaman lafiya kamar yadda ta saba.

Babban Mai Ba Gwamna Bala Mohammed Shawara Kan Harkokin Watsa Labarai, Mukhtari Gidado, ya shaida wa Aminiya cewar Sarkin ya rubuto wa gwamnati takardar ban hakuri kamar yadda kwamitin binciken ya bukata kafin aka dawo da shi.

Ana ganin dage dakatarwar ya dawo da martabar masarautar, wadda kananan hukumomin Misau da Dambam na jihar ke karkashinta.