✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin APC ta gaza a Katsina – Jikamshi

Alhaji Abubakar Halilu Jikamshi, shi ne dan takarar Gwamnan Jihar Katsina a karkashin Jam’iyyar NRM, ya yi ritayi a matsayin Babban Darakta a Hukumar Birnin…

Alhaji Abubakar Halilu Jikamshi, shi ne dan takarar Gwamnan Jihar Katsina a karkashin Jam’iyyar NRM, ya yi ritayi a matsayin Babban Darakta a Hukumar Birnin Tarayya Abuja. Tsohon Mataimakin Shugaban Kungiyar Masana Filaye da Safiyo ta Kasa, a  tattaunawarsa da Aminiya ya ce gwamnatin jihar ta gaza tabuka abin a zo a gani. Sannan ya ce Katsina za ta fi kowace jihar samun ribar dimokuradiyya idan aka zabe shi Gwamnan Jihar a bana:


Aminiya: Da farko idan Allah Ya sa ka zama Gwamnan Jihar Katsina, me za ka yi wanda zai bambanta da yanayin da ake ciki a jihar?

Da farko, zan yi aiki da masu son ci gaba, don inganta rayuwar al’ummar jihar wadanda za mu yi aiki tare don bunkasa harkokin tattalin arziki ta hanyar kafa masana’antu da janyo hankalin masu zuba jari su kafa kamfanoni ta yadda za a samar wa matasanmu ayyukan yi. Domin a kullum muna horar da dalibai daga makarantun sakandare da jami’o’i to amma babu ayyukan yi.

Ina zaune a Abuja amma na san yadda takwarorinmu na Kudu suke gudanar da harkokinsu. Wadansu gwamnonin Kudancin Najeriya suna yi wa jama’arsu aiki tukuru don samar da filayen gina masana’antu wanda hakan zai taimaka wajen rage rashin ayyukan yi wannan yana daya daga cikin burinmu a Katsina. Sannan Katsina Allah Ya albarkace ta da ma’adinai ga kuma kasar noma, wanda wannan gwamnati ta gaza mai da hankali a kansu. Sai ya zama jiya i yau, babu ci gaba. Kuma idan ka duba yawanci rashin aikin yi ga matasan nan ne ke haddasa mafi yawan tashe-tashen hankula da sauran fitinu na Boko Haram da satar mutane da bangar siyasa.

Wadanne tsare-tsare za ka fito da su don cimma wannan kudiri?

Za mu gayyaci wadanda suka dace don tabbatar da ba a dogara da kason kudin tarayya ba. Za mu fuskanci harkokin ilimi da noma da samar da ayyukan yi. Mu mayar da matasanmu abin alfahari, domin suna da fasaha, amma an ki ba su dama. Sannan za mu janyo hankali masu zuba jari zuwa Katsina don sarrafa albarkatun da muke da su na ma’adinai da harkokin noma.

Jam’iyyarka na cikin sababbin jam’iyyun da aka yi wa rajista da za ta tunkari APC a Katsina, wace dama NRM ke da shi na samun nasara a zaben?

Taken jam’iyyarmu shi ne ‘Allah ke ba da mulki’ kuma mun yarda cewa, Allah ke ba da mulki lokacin da Ya so ga wanda Ya  so. Kuma zai iya hana kowa duk dukiyar da mutum ya mallaka ko jama’a. Kuma manufarmu ita ce mu yi wa jama’a hidima. A mako mai zauwa zan kaddamar da yakin neman zabena a Katsina, inda za mu hada kai da dukan masu kishin jihar don tabbatar da mun kai ga nasara. Domin kowa shaida ne cewa APC a Katsina ta gaza kan manufofi da kudurin da al’umma suka zabe ta a kansu. Ai da muna cikinta, tun a ANPP har muka zo APC, amma abin takaici sai ya kasance sauyin da al’umma ke zaton samu bai yiwu ba, wannan ne dalilin da muka kafa wannan jam’iyya a karkashin jagorancin Sanata Dansadau don ceto kasar nan daga halin da ta ke ciki ba jihar Katsina kawai ba.

Jihar Katsina jihar Shugaban Kasa Buhari ce, da jam’iyyarsa ke mulkin jihar. Ta ina za ka fuskanci wannan kalubale don ganin ka samu nasara a zaben bana?

Hakika faduwar Buhari a wannan takarar ba karamin aiki ba ne, saboda irin kaunar da jama’ar jihar suke yi masa, amma a zahiri da a ce ana yin dimokuradiyya irin ta kasashen da suka ci gaba ba abu ba ne mai wahala kayar da shi, ba shi karan kansa, balle sauransu. Gwamnatin ta gaza ta fannoni da dama. ’Yan Najeriya suna cikin wahala, jama’a ba sa tsammanin abin da suke fuskanta a yanzu na wahalhalun rayuwa da rashin tsaro. Abin mamakin shi ne Ministan Tsaro  dan Arewa maso Yamma ne, amma har yanzu ban san me yake yi a kan munanan ayyukan ta’addanci da suke faruwa a kasar nan ba.

Jama’ar Jihar Katsina suna cewa, yana biya musu bukatunsu. Me ya sa kake kalubalantarsa a wannan karo?

Ba zan iya cewa, bai tabuka  komai ba. A tunanina yana daya daga cikin mutanen da suka sa Buhari ya gaza. Ya kamata ka ziyarci Jihar Katsina ka saurari koke-koken talakawan jihar. Ana bukatar wayar da kan al’umma don fitar da su daga kangin wahalar da suke ciki a yanzu. Jihar Katsina na cikin jihohin da ke da masu ilimi a kasar nan, mafi yawan tsofaffin shugabanninmu daga nan suke, amma ba inda muka dosa har yanzu.

da yanayin da matasa za su samu ayyukan yi. Ba a horar da su akan su samu wasu dama da zasu iya dogara da kansu, sai dai kawai muna samar da kofa ga masu nishadantarwa kawai.

Akwai bukatar ka zauna a Jihar Katsina don ka san halin da jama’ar jihar ke ciki. Ba su kokarin magance rashin aikin yin ga matasa daga tushe, wanda ya bai wa ’yan Boko Haram kofar horar da mambobinsu. Ba a kama wadanda suke taimaka musu.

Kana da yakinin Hukumar INEC za ta iya gudanar da sahihin zabe a bana?

Ina fatar haka, saboda an yi min magudi lokacin da nake takara. Na san abin da hukumar zaben za ta iya aiwatarwa da hukuncin da za su iya yankewa. Ina farin ciki cewa, Babban Jojin Najeriya Mai shari`a Ononghen ya gargadi  alkalai su zage damtse a ayyukansu, kuma muna da yakinin cewa za su yi adalci a zabe na gaba.

Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya yi alkawarin cewa, hukumar za ta gudanar da sahihin zabe, saboda an samu darasi daga zabubbukan jihohin Osun da Ekiti.

Ka gamsu da yadda Jam’iyyar NRM ke karbuwa a Katsina?

Jama’a da dama na ta sauya jam’iyya, amma masu fada-a-ji ba sa shigo wa jam’iyyarmu, saboda su a tunaninsu ta hanyar gwamnati ce kadai za su iya samun kudi. Wadannan mutanen ba sa amfani da tunaninsu, sukan manta da ranar tashin Kiyama. Duk mabiyanmu da suka halarci kamfen dinmu a Gusau za su hallara a Katsina, wannan zai nuna yadda jama’a ke goyon bayanmu kuma hakan zai nuna cewa a shirye suke da kawo sauyi.