Wata ’yar fafutikar kare hakkin mutanen yankin Neja-Delta, Misis Annkio Briggs ta zargi gwamnatin Jam’iyyar APC da kashe tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa Cif Diepreye Alamieyeseigha.
Misis Briggs ta ce Alamieyeseigha ya rasu ne sakamakon tsorata shi da kuma firgita shi sakamakon yunkurin gwamnatin Birtaniya na baya-bayan nan na mayar da shi Landan don fuskantar tuhuma kan zargin cin hanci da rashawa.
Ta yi bayanin cewa, tsohon Gwamnan yana waje a Dubai domin duba lafiyarsa lokacin da rahotanni suka bayyana cewa ana yunkuri iza keyarsa zuwa Ingila. “Akwai shirin kama shi a Dubai, don haka ya dawo Najeriya ba shiri. Kuma yana dawowa hukumomin Gwamnatin Tarayya suka addabe shi har ya fara rashin lafiya. Gwamnatin Tarayya ta yi wa Alamieyeseigha afuwa ya rasa kusan daukaci dukiyarsa, amma duk da haka sai da suka hada baki da gwamnatin Birtaniya don iza keyarsa kan lamarin da aka riga aka gama magana a kansa,” inji ta.
’Yar gwagwarmayar ta ce Gwamnatin Tarayya tana kashe ’yan kabilar Ijaw a hankali ta hanyar cusa musu bakin ciki. “Sun samu nasarar kashe Alamieyeseigha yanzu kuma suna matsa wa Diezani, amma ba za su samu nasara ba,” inji ta.
Misis Briggs ta ce akwai mahandaman ’yan Najeriya da dama da suka sace dukiyar kasar nan da suke yawonsu ba tare da tsangwama ba, don haka ’yan kabilar Ijaw ba za su zauna su zuba ido ana kokarin kashe su ba.
Sai dai a martanin da Jam’iyyar APC reshen Jihar Bayelsa ta mayar ta ce da’awar wasu ’ya’yan Jam’iyyar PDP suka yi cewa APC tana da hannu a mutuwar Alaimeiseigha a matsayin abin kunya.
Wata sanarwa daga Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar a Jihar, Fortune Panebi ta ce wannan muguwar siyasa da PDP ta bullo da ita wani yunkuri ne na kawar da hankalin gwamnati mai ci daga mummunan tabarbarewar da harkokin kiwon lafiya yake ciki a jihar duk da biliyoyin Naira da gwamnatin Seriake Dickson ta kashe da sunan gyara kayayyakin kiwon lafiya.
A cewar APC “Abin bakin ciki ne mutanen da Alaimeiseigha ya ceto daga raga za su yi watsi da shi a lokacin da yake fama da rashin lafiya, saboda ya ki fitowa fili ya bayyana goyon baya ga tazarcen Mista Dickson.
Gwamnatin APC ce ta kashe Alamieyeseigha – Briggs
Wata ’yar fafutikar kare hakkin mutanen yankin Neja-Delta, Misis Annkio Briggs ta zargi gwamnatin Jam’iyyar APC da kashe tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa Cif Diepreye Alamieyeseigha.Misis…