✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Abba za ta dora a kan ayyukan Ganduje —Kwankwaso

Kwankwaso ya bayyana abin da suka tattauna da Tinubu da kuma bangarorin da Gwamna Abba zai ba wa muhimmaci

Jagoran Jam’iyyar NNPP, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf za ta yi duba tare da kammala ayyukan da Gwamnatin Ganduje ba ta kammala ba a Jihar Kano.

A hirarsa da wasu kafofin yada labarai a Kano a jajibirin rantsar da Abba a matsayin gwamna, Kwankwaso ya bayyana cewa “Na tabbatar wannan gwamnati za ta yi duba ga ayyuka masu amfani ga al’umma ta karasa su, mu ba za mu bari adawa ta hana mu gudanar da ayyuka na ci gaban alumma ba.”

Ya kuma yi kira ga wadanda za a ba wa mukaman gwamnati a sabuwar gwamnatin da su sani cewa aiki za su yi tukuru ba wai satar dukiyar al’ummar ba.

“Duk wani da za a ba mukami ya sani cewa aiki zai zo ya yi wa alummar Jihar Kano ba wai kwashe kudi ba,” in ji shi.

A cewarsa, “Mun ga yadda wadannan barayin maciya amana suka sace kudin alummar Jihar Kano; Idan ka duba su ke da otel-otel din da ke Kano da manya-manyan filaye, to ba za mu yarda mu maimaita irin abin da suka yi ba.”

Ya kara da cewa gwamnatin Abba za ta mayar da hankali ga bangaren ilimi duba da wofintar da bangaren da gwamnatin Ganduje ta yi.

“Kowa ya san halin da makarantun Jihar Kano ke ciki. Duk makarantun da muka kirkira an banzatar da su sun zama kufai.

“Wasu makarantunmu suna nan a yadda muka bar su ko bulo daya ba a kara musu ba, yayin da wasu kuma aka daina harkar koyarwa a cikinsu gaba daya,” in ji Kwankwaso

Ya ba da tabbacin cewa zababben Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf zai yi iya kokarinsa wajen samar wa matasan jihar ayyukan yi da za su dogara da kansu tare da raba su da harkar shaye-shayen muggan kwayoyi.

Ya kuma roki al’ummar Jihar Kano su taya gwamnatin da addu’a don ganin an gudanar da ayyuka masu inganci.

Sabbin masarauu

Kwankwaso ya jaddada cewa gwamnati mai shigowa za ta yi nazari a kan masarautun Kano da Gwannatin Ganduje ta kirkira.

“Muna da kyakkyawar alaka da dukkanin sarakunan da ke Masarautun Kano, ba kamar yadda wasu ke zargi ba .

“Wannan batu da ake yi na rushe ko barin sabbin masarautu abu ne da sai gwamnati ta zo ta zauna ta yi nazari a kai,” in ji shi.

Ganawa da Tinubu

Da yake jawabi game da tattaunawarsa da zababben shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a Faransa, wadda da ta dau hankalin jama’a , Kwankwaso ya bayyana cewa sun tattauna ne a kan yadda za a shawo kan abubuwan da suka addabi Najeriya.