Nakasasssu a Adamawa sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta ba su damar su ma a dama su a harkokina.
Shugaban kungiyar nakasassu a jihar, Sani Sabo ne ya bayyana hakan a wajen wani taron yini daya da aka shirya karkashin daukar nauyin cibiyar USAID.
- MURIC Ta Yi Tir Da Taron INEC A Coci
- NAJERIYA A YAU: Yadda Dokar Rage Cire Kudi a POS Za Ta Shafi Zaben 2023
Sabo ya ce, duk da cewa gwamnatin jihar ta san da zamansu, sai dai babu kulawar da suke samu daga gare ta, ballantana yi da su a harkokinta.
Ya kara da cewa, suna da tarin gudunmawar za su bayar don ci gaban jihar da ma kasa baki daya.
A ranar Alhamis ce aka shirya taron albarkacin Ranar Nakasassu ta Duniya.
Taron, ya bukaci mahalartansa da su yi amfani da darussan da suka koya wajen inganta rayuwarsu da ta al’umar da suke cikinta.
(NAN)