✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta yi watsi da dokar kula da lafiyar yara kyauta

Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, ya ce a gwamnati ba ta da kudin kula da lafiyar kananan yara kyauta

Gwamnatin Tarayya ta yi fatali da kudurin Dokar Kula da Kafiyar Kananan Yara kyauta a fadin Najeriya.

Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, ya ce gwamnati ba za ta iya kula da lafiyar kananan yara a kyauta ba, duba da matsin tattalin arziki da Najeriya take ciki.

Ya ce maimakon kula da lafiyar yara kyauta: “Kamata ya yi a kara wayar da kan jama’a a yi wa kowane yaro rajista a shirin inshorar lafiya a matakai daban-daban domin samun kula da lafiyarsu a kan farashi mai rahusa.”

Ehanire, ta bakin Daraktar Sashen Samar da Magungunan Daga Tsirrai, Zainab Shariff, ya kuma yi watsi da wasu kudurorin doka hudu da Majalisar Wakilai ta gabatar a bangaren lafiya.

A bayaninsa ga taron sauraron ra’ayoyin jama’a kan sabbin dokokin da Majalisar Wakilai ke aiki a kai a Abuja, Ministan ya ce, “Kafa sabbin hukumomin lafiyar da majalisar ta ke so barnar kudi, domin ayyukansu za su ci karo da na hukumomin da ake da su a yanzu.”

A yayin bude taron, Shugaban Majalsiar Wakilai, Femi Gbajabiamila, wanda Mataimakiyar Mai Tsawatarwar Majalisar, Nkeiruka Onyejeocha ta wakilta, ya ce Majalisar ta yi kudurorin ne saboda muhimmancin da ta bayar ga bangaren lafiya da ma’aikatan bangaren.

Cin karo da juna

Kudurorin hudu dai na bukatar in gyaran fuska ga wasu dokokin da suka shafi ayyukan hukumomin lafiya a karkashin ma’aikatar.

Amma Ehanire ya bayyana cewa dokar kayyade mafi karancin sharudan kafa cibiyoyin lafiya ba ta da wani amfani domin ma’aikatar ta yi gagarumin aiki a bangaren ta wasu hanyoyin daban-daban.

Sannan ya ce kudurin dokar kafa cibiyoyin wanke guba da gurbatattun abubuwa a jihohi 36 da kuma Abuja abu ne da zai ja wa gwamnati karin kashe kudade.

Kudurin dokar Hukumar Kula da Masu Sayar da Kayan Abinci kuma, a cewarsa, zai ci karo da wasu dokoki da kuma ayyukan wasu hukumomin gwamnati.

Kuduri na hudu shi ne na dokar kafa Hukumar Kula da Ma’aikatan Kula da Lafiyar Al’umma.

Amma ministan ya ce ayyukan sabuwar hukumar za su ci karo da ayyukan Cibiyar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa da Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko da kuma Cibiyar Kula da Jami’an Lafiya ta Afirka.