Gwamnatin Najeriya ta yi wa daliban Najeriya da ke karatu a kasar Ukraine kafin mamayar Rasha tayin ba su guraben karatu a jami’o’in Najeriya duk da yajin aikin da malaman jami’o’i ke ci gaba da yi a kasar.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ce ta sanar da shirye-shiryenta na mayar da daliban da ke karatu a kasar ta Ukraine a cikin wata sanarwa.
- Mun kashe ’Yan Najeriya 38 da ke taimakon Ukraine a yaki —Rasha
- Buhari ya ba Yobe tallafin hatsi ton 360
Ma’aikatar ta ce tuni shirye-shirye suka yi nisa don ganin an sama wa wadannan dalibai guraben karatu a jami’o’in gwamnati.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da mai magana da yawun Ma’aikatar, Francisca K. Omayuli, ta sanyawa hannu a ranar Litinin, hudu ga Yulin 2022.
Sanarwar ta ce dalibai masu sha’awar ci gaba da karatun a gida su hanzarta ziyartar shafin ma’aikatar domin cike bayanansu ta intanet kafin ranar 15 ga watan Yulin da muke ciki.
A halin yanzu, kimanin watanni biyar ke nan Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta tsuduma yajin aiki wanda har yanzu ba a san ranar dawowarta ba.
Tun bayan da Rasha ta kaddamar da yaki a kasar Ukraine dai, miliyoyin mutane, ciki har da daliban Najeriya da ke karatu a can, suka bar kasar bayan sun yi gudun hijira.
Tun lokacin ne dai karatun nasu ya sami tsaiko, kuma ba su san ranar komawar su ba don ci gaba da karatun.