Biyo bayan ficewar Ƙungiyar ƙwadago da ta ‘yan kasuwa a zaman da suka yi da kwamitin da aka yi kan mafi ƙarancin albashi rahotanni sun gano cewa gwamnatin a yanzu ta kara daga ya kai N54,000.
Wata majiya mai tushe a cikin taron da ke gudana a halin yanzu ta bayyana hakan ga majiyar jaridar PUNCH a Abuja.
“A yanzu gwamnatin tarayya ta gabatar da ƙudirin Naira 54,000,” in ji majiya mai tushe.
- Hayaƙin janareta ya kashe dalibai 7 a Bayelsa
- Majalisar Kano za ta yi wa dokar masaratu gyaran fuska
Kodayake ba a bayyana ko ‘yan Ƙwadagon za su amince da wannan tayin ba, The PUNCH ta ruwaito cewa shawarar gwamnatin tarayya ta yi nisa daga N615,000 da ƙungiyar ƙwadago ta gabatar.
Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya, Joe Ajaero, ya dage kan biyan mafi ƙarancin albashi na N615,000, yana mai cewa sun zabi hakan ne bayan nazarin halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki da kuma buƙatun talakawa ga mai iyali mutum shida.
Ya zargi gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu kan taɓarɓarewar tattaunawar, yana mai cewa, “Duk da ƙoƙarin da ake na cimma yarjejeniya ta gaskiya, matakin da bai dace ba na gwamnati da Ƙungiyoyi masu zaman kansu ya haifar da rugujewar tattaunawar.
Amma da yake magana a madadin kungiyoyi masu zaman kansu, Darakta-Janar na ƙungiyar tuntubar ma’aikata ta Najeriya, Mista Adewale-Smatt Oyerinde, ya bayyana tafiyar ƙungiyoyin a lokacin da ba a fara tattaunawa a matsayin abin takaici.