✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Gwamnati ta binciki yunkurin kashe Gwamnan Borno’

Ya kamata gwamnatin ta yi cikakken bincike kan yunkurin kashe Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum

An bukaci Gwamnatin Tarayya da ta kafa kwamitin bincike mai zaman kansa kan yunkurin kashe Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum.

A ranar Laraba wasu mayaka da ake zaton ‘yan Boko Haram ne sun yi barin wuta a kan tawagar motocin gwamnan a hanyarsa ta zuwa Kananan Hukumomin Monguno da Kukawa a jihar.

A ranar Talata ne ake sa ran Kungiyar Gwamnoni ta Najeriya za ta gana da Shugaba Buhari ka harin da aka kai wa gwamnan, kamar yadda shugaban kungiyar Gwamna Kayode Fayemi na Ekiti ya sanar a wasikar jajen kungiyar ga Zulum da jama’ar Borno.

Mai bayar da shawara na musamman ga gwamnan kan kasuwanci da zuba jari, Bashir Maidugu ya ce, “Muna zargin harin da aka kai wa motocin Gwamna a Baga yunkuri ne da halaka shi.

“Muna kiran Gwamnatin Tarayya ta yi nata binciken mai zaman kansa”, inji shi, a hirarsa da wakilinmu ta waya.

Ya ce gwamnan ya tsallake rijiya da baya a hannun masu neman kashe shi.

An kuma yi harbi a kan motocinsa a lokacin da yake wucewa yankin Nganzai da ke cikin Maiduguri.

Maidugu ya ce gwamnan ya yi tafiyar ne bayan samun tabbaci daga sojoji, don haka ya kama Gwamnatin Tarayya ta yi nata binciken kan lamarin.

A harin na baga, akalla jami’an tsaro biyu sun samun raunuka a harinn Baga.

A nasa bangaren, Gwamna Zulum, yayin karbar bakuncin gwamnonin jam’iyyar APC da suka kai masa ziyarar jaje ya yi zargin wata makarkashi na neman hana kawo karshen ayyukan Boko Haram a jiharsa.

Gabanin nan, Shehun Borno Alhaji Abubakar Umar Ibn Garbai Elkanemi ya ce harin ya nuna babu wanda ya fi karfin ayyukan kungiyar a jihar ke nan.

Mai Magana da Yawun Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Kanar Sagir Musa, ya ce rundunar ta fara bincike kan harin da aka kai wa gwamnan.