Gwamnatin Tarayya ta ba kamfanonin sadarwa umarnin hana duk layukan wayar da ba a hada su da lambar NIN ba yin kira da layukansu daga ranar Litinin.
Kamfanonin da umarnin ya shafa sun hada da MTN da Globacom da Airtel da kuma 9mobile.
- ’Yan bindiga sun kashe dan Kwamishinan Tsaron Zamfara
- ‘Sharrin Shaidan ne ya sa na kona matata da kaninta’
Tun a watan Disamban 2020 ne Gwamnatin Tarayya ta umarci kamfanonin sadarwa su tilasta wa dukkan masu amfani da layuka a Najeriya bhada lambobinsu da Lambar Zama dan Kasa (NIN) a matsayin bangaren inganta tsaron kasa.
A baya dai an sha dage wa’adin a lokuta daban-daban, inda a dagewa ta karshe aka sanya ranar 31 ga watan Maris din da ya gabata.
Amma a cikin wata sanarwa ranar Litinin, Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, ya umarci dukkan kamfanonin da su kulle layukan da suka yi kunnen kashe daga ranar Litinin, hudu ga watan Afrilun 2022.
Pantami ya ce matakin na daga cikin tanade-tanaden aiwatar da dokar hada layukan da lambobin NIN.
Sanarwar dai, wacce ta hadin gwiwa ce na dauke da sa hannun mai magana da yawun Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC), Ikechukwu Adinde, da takwaransa na Hukumar Kula da Katin Zama dan Kasa (NIMC), Kayode Adegoke.
Ministan ya ce ya zuwa ranar Litinin, akalla layuka miliyan 125 ne suka mika lambobin NIN din nasu don a hada, yayin da ita kuma hukumar NIMC ta yi wa mutum miliyan 78 rajista.