Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin, 12 ga watan Yuni, a matsayin ranar hutu albarkacin Ranar Dimokuradiyya ta bana.
Babban Sakataren Ma’aikatar Al’amuran Cikin Gida, Dokta Oluwatoyin Akinlade, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Alhamis.
- BIDIYO: Shekara 25 da rasuwar tsohon Shugaban Najeriya Sani Abacha
- Rikicin Shugabanci: ’Yan sanda sun rufe majalisar dokokin Nasarawa
Baya ga taya ’yan Najeriya murna, sanarwar ta ce kamar sauran kasashe, Dimokuradiyyar Najeriya ta yi fama da nasarori da kuma tarin kalubale.
Ta kuma ce, “Amma babban abin birgewar shi ne Najeriya, a matsayinta na kasa da kuma mutanenta sun tsaya tsayin daka wajen ganin ginshikan Dimokuradiyya sun tabbata.
“A wannan rana mai cike da tarihi, muna gayyatar ’yan Najeriya da kawayen kasar su zo su taya mu murnar ci gaban da muka samu sannan a duba hanyoyin da za abi wajen ciyar da Dimokuradiyyar gaba,” in ji sanarwar.
Tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ne dai ya sauya ranar Dimokuradiyyar zuwa ranar ta 12 ga watan Yuni.
A baya dai, ana bikin ne a ranar 29 ga watan Mayu.