✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta amince ta bai wa mahajjata kuɗin guzirinsu a hannu

Hukumar NAHCON ta dage cewa ɓullo da hada-hadar kuɗi ta amfani da kati zai shafi shirin hukumar na gudanar da ayyukan hajjin 2025.

Gwamnatin Najeriya ta amince kuma ta sanar cewa za a bai wa mahajjatan ƙasar kuɗin guzirinsu a hannu maimakon amfani da kati ko kuma asusun banki.

Hakan ya biyo bayan tsoma bakin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi wanda ya roƙi shugaba Bola Tinubu a madadin maniyyatan ta hannun Hukumar Alhazai ta Ƙasa NAHCON.

Hukumar NAHCON a ƙarƙashin jagorancin Farfesa Abdullahi Saleh, ta dage cewa ɓullo da hada-hadar kuɗi ta amfani da kati zai shafi shirin hukumar na gudanar da ayyukan hajjin 2025.

Shugaban ya damu matuƙa da cewa amfani da katin banki na dole da babban Bankin Najeriya  CBN ya gabatar don gudanar da aikin hajji zai kawo tarnaƙi ga tsare-tsare da kuma gudanar da aikin Hajjin bana na 2025.

Bayan ganawar Hukumar NAHCON da Mataimakin shugaban ƙasa,  Kwamishinan tsare-tsare da ayyukan kuɗi na NAHCON, Aliu Abdulrazaƙ, na cewa hakan zai bai wa mahajjan Najeriya damar kashe kuɗaɗensu da hannunsu yayin ibadar a Saudiyya.