Gwamnatin kasar Sudan da ’yan tawayen kasar masu dauke da makamai sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya ta karshe a ranar Asabar.
Gidan talabijin din kasar ya watsa yadda bikin sa hannun ya gudana kai tsaye wanda aka yi a babban birnin Sudan ta Kudu, Juba.
Mataimakin Shugaban Majalisar Kolin kasar Sudan, Mohamed Hamdan Daqlu, shi ne ya rattaba hannu a madadin Gwamnatin kasarsa a yarjejeniyar wadda kungiyar ’yan tawaye ta Revolutionary Front Alliance ta jagoranci sauran kungiyoyin masu dauke da makamai wajen sa hannu.
Mahalarta taron sun hada da Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu; Shugaban Majalisar Kolin kasar Sudan, Abdel Fattah Al-Burhan; Firaministan Sudan, Abdalla Hamdok.
Sauran sun hada da wakilan kasashen Saudiya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Qatar, Masar da kuma Chadi.
Kazalika, taron ya karbi bakuncin wakilan kungiyoyin sassa da kuma na kasa da kasa ciki har da Majalisar Dinkin Duniya, Tarayyar Afirka, Kungiyar Kasashen Larabawa, da kuma Tarayyar Turai.
Kasar Sudan dai ta yi ta fama da rikice-rikicen siyasa tun bayan hambarar da gwamnatin Shugaba Omar Al-Bashir da aka yi a bara.