✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnan Yobe ya yi wa ‘yan kasuwa ragin kudin shaguna

Buni ya dauki wannan mataki ne domin karfafa kasuwanci a jihar

Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya yi wa ‘yan kasuwar da ke zaune a sabuwar kasuwar zamanin da ya kaddamar ragin kashi 35 cikin 100 na kudin shaguna.

Gwamnan ya dauki wannan mataki ne domin karfafa wa ‘yan kasuwar da kuma bunkasa harkar kasuwanci a jihar.

Majiyarmu ta nuna shagunan da aka yanke wa N468,000 da farko, yanzu N304,200 za a biya a shekara, na N390,000 kuwa a biya N253,500.

Haka nan, shagunan N442,000 sun koma N287,300, yayin da na N390,000 sun koma N253,500 a shekara.

Sai kuma shagunan N325,000 da a yanzu suka koma N211,250, kana na N253,500 za a biya N390,000 a kansu a shekara.

Sashen da za a biya N390,000, yanzu sun koma N253,500, sannan na N325,000 a biya N211,250 da N236,600 a shekara.

Bangaren ‘yan N169,000 kuwa yanzu N152,100 za a biya, na N260,000 a biya N169,000, na N325,000 a biya N211,250 duk a shekara.

Sauran sun hada da shaguna ‘yan N286,000 inda za a biya N185,900, na N325,000 a biya N211,250, sai kuma shagunan N162,500 inda a yanzu aka yi rangwame a biya N105,625.