✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Yobe ya yi alhinin mutuwar diyar Wamakko

Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, ya jajanta tare da mika sakon ta’aziyyarsa ga tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko wanda diyarsa, Sadiya…

Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, ya jajanta tare da mika sakon ta’aziyyarsa ga tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko wanda diyarsa, Sadiya ta koma ga Mahallicinta.

Cikin sanarwar da Buni ya fitar a ranar Asabar ta hannun mai magana da yawunsa, Mamman Muhammad, ya misalta mutuwar Sadiya a matsayin babban rashi ga dukkan dangi, makusanta, da ‘yan uwa da kuma Najeriya baki daya.

Buni wanda kuma shi ne shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC, ya yi addu’ar Allah ya yafe kura-kuranta, ya kuma sa Aljannar Firdausi ce makoma.

Mai Mala ya kuma yi addu’ar neman Mai Duka ya ba wa Sanata Wamakko da iyalansa hakuri da juriyar rashin da suka yi.

Sanata Wamakko wanda yake wakilcin shiyyar Sakkwato ta Arewa a zauren Majalisar Dattawa, ya rasa diyarsa ne a ranar Alhamis tana da shekaru 23 kacal a duniya.

Marigayiya Sadiya ta yi gamo da ajali a asibitin koyarwa na Jami’ar Usman Danfodiyo da ke birnin Shehu bayan ta samu tangarda yayin haihuwa.