Gwamnatin Jihar Nasarawa ta umarci hukumomin tsaro a jihar su gaggauta gudanar da bincike domin kamo tare da hukunta wani jami’in Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar mai suna Muhammed Sangir da ake zargi da damfarar miniyyata aikin Hajjin bana 15 daga jihar.
Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura ne ya ba da umarnin a jawabinsa na ban-kwana ga maniyyatan jihar a Lafiya, inda ya ce wanda ake zargin ya karbi kudin kujerun mutum 15 ba tare da sanin hukumar ba, kuma ya tsere bayan ya samu labarin cewa jami’an tsaro suna nemansa.
Gwamnan ya ce an gano haka ne bayan da hukumar ta tantance wadanda ta karbi kudin kujera a wurinsu kafin su tashi tafiya zuwa kasa Mai tsarki inda ta gano cewa maniyyatan 15 ba sunansu cikin wadanda suka biya kudin kujerunsu, inda hakan ya sa ta gudanar da bincike ta gano cewa maniyyatan sun ba wanda ake zargin ne kudin.
Gwamna Al-Makura, ya jajanta wa wadanda lamarin ya shafa kan rasa zuwa kasa Mai tsarkin, inda ya tabbatar musu cewa gwamnatin jihar da ta tarayya da hadin gwiwar hukumomin tsaro za su gudanar da cikakken bincike cikin gaggawa a kan lamarin su kuma kamo wanda ake zargin a karbo musu kudinsu don ba su damar cika burinsu na tafiya aikin Hajji a nan gaba.
Kakakin Hukumar, Abdurrazak Mohammed ya shaida wa wakilinmu cewa bayan maniyyatan da lamarin ya shafa sun kai korafinsu ga hukumar cewa ba su ga sunayensu a cikin wadanda suka biya kudinsu ba alhali sun bai wa wanda ake zargin wato Muhammed Sangir ne sai hukumar ta gudanar da bincike inda ta gano cewa wanda ake zargin ya karbi kudin maniyyatan amma bai sa a asusun hukumar ba.
A cewarsa wanda ake zargin ya gudu a lokacin da ake bincike a kan lamarin, inda ya shawarci maniyyata su rika biya kudin kujerarsu ga hukumar kai-tsaye su daina bai wa jami’an hukumar komai matsayinsu in ba wanda hukumar ta ajiye don haka ba, domin kauce wa sake aukuwar haka nan gaba.
Maniyyatan da lamarin ya shafa sun nuna takaicinsu kan lamarin inda suka nuna damuwa kan yadda wanda ake zargin ya damfare su alhali yana aiki da hukumar.
Gwamnan Nasarawa ya umarci a gaggauta kamo jami’in da ya damfari maniyyata 15
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta umarci hukumomin tsaro a jihar su gaggauta gudanar da bincike domin kamo tare da hukunta wani jami’in Hukumar Jin Dadin Alhazai…