Gwamnan jihar Legas, Babajide, Sanwo-Olu ya kamu da cutar Coronavirus wacce aka fi sani da COVID-19.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Farfesa Akin Abayomi ne ya tabbatar da kamuwar gwamnan da annobar ranar Asabar, inda ya ce an tabbatar da ganin alamar farko ta rashin samun kuzari da ta fara bayyana a jikinsa.
- Coronavirus: Gwamnan Legas ya yi addu’ar Easter a gida
- Mai gidan jaridar Leadership, Sam Nda-Isaiah ya rasu
- COVID-19 ta sake bulla a Kano, ta kashe mutum biyu
Kwamishinan ya ce, “Mai girma gwamnan yana kan karbar magani kuma yana samun kulawa a gida daga kwararrun ma’aikatan yakar cutar COVID-19 na IDH Yaba.
“Tun da Mista Sanwo-Olu ya fara karbar magani tare da hutu ya ke samun sauki, kuma ana sa ran zai warke cikin gaggawa.
“Akwai karuwar masu kamuwa da cutar COVID-19 a wasu wurare a Legas, saboda haka muna baiwa mutane – baki da ‘yan gari – shawarar su bi shuruddan da hukumomin lafiya suka gindaya na kariya daga cutar kamar sanya takunkumin fuska da wanke hannu, da kuma kaucewa shiga cunkoson jama’a,” inji Abayomi