✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Kuros Riva ya biya wa mutum 15 kudin hajji

Kimanin mutum 30 za su sauke farali a aikin hajjin  bana duk kuwa da irin ’yan matsaloli na tsada da kuma rashin isassun kudi a…

Kimanin mutum 30 za su sauke farali a aikin hajjin  bana duk kuwa da irin ’yan matsaloli na tsada da kuma rashin isassun kudi a hannun jama’a, sai dai mutum 15 ne suka biya kudi yayin da sauran 15 kuma Gwamnan Jihar Kuros Riba Sanata Farfesa benedict Ayade ne ya biya musu.

Alhaji Tanimu Hassan shugaban hukumar Alhazai ta Jihar Kuros Riba ne ya sanar da haka a hirarsa da Aminiya. da aka tambayeshi ko akwai wadanda suka bayar da kudin ajiya kafin su cika sauran suka  kasa cikawa “eh! Mutum daya ne kuma tuni an mayar masa da kudinsa yanzu dai mutum 30 ne daga Kuros Riba in Allah ya yarda za su tafi aikin hajji na bana,”inji shi.

A cewar Alhaji Hassan: “Gwamna ma ya ba mu hakuri, inda ya ce in Allah ya yarda shekara mai zuwa zai dauki nauyin mutum 50 ko 100 ma.” Sakamakon irin yadda wannan shekarar   ta zo wa kowa da wani irin yanayi ne ya sanya ba a samu yawaitar matafiya ba. Amma “gwamna ya yi alkawari daga shekara mai zuwa in Allah ya yarda zai iya daukar nauyin mutum 50 zuwa 100.” 

karshe ya jadda alkawarin da ya yi shugaban hukumar alhazan na “a wannan lokaci na shugabancina insha Allah ba za a samu korafin zalunci ko karkata kudin maniyyaci don son zuciya ba, zan  kamanta gaskiya da adalci.” Ya yi fata ’yan Najeriya da ma al’ummar Kuros Riba za su ci gaba da taya shi da addu’a. Gwamnatin Jihar Kuros Riba  ta nada barista Musa Abdullahi Maigoro mataimaki na musamman kan harkokin baki matsayin Amirul-Hajj na jihar.