Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya haramta harkokin kungiyoyin kwadago a makarantun gwamnatin jihar.
Bello wanda ya bayyana haramcin jiya ya ce gwamnati ta dauki matakin ne sakamakon yajin aikin ba-gaira-ba-dalili da gamayyar kungiyoyin kwadagon suke shirin yi.
Makarantun da haramcin ya shafa sun hada da kwalejin kimiya da fasaha da ke Lakwaja da Kwalejin Horan Malamai da ke Ankpa da Kwalejin Horan Malaman Kimiyya da ke Kabba da Kwalejin Koyon Ingozoma da Rainon Ciki da ke Obangede da Kwalejin Koyon Jinya da Kimiyya ta Idah da Jami’ar Asibitin Kwararru da ke Anyigba.