Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Yahaya Bello na Jam’iyyar APC a zaben Gwamnan Jihar Kogi na ranar 16 ga watan Nuwamban 2019.
A safiyar Litinin alkalan Kotun guda bakwai suka sun yi watsi da daukaka karar da dan takarar Jam’iyyar PDP a zaben, Musa Idris ya yi bisa zargin cewa Yahaya Bello bai ci zaben ba.
Alkalin da ta jagoranci zaman, Uwani Abba-Aji, ta ce masu daukaka karar sun kasa tabbatar da zarge-zargen da suka daukaka karar a kai.
Musa Idris na zargin an yi rikicin siyasa a zaben, na’urar tantance masu zabe ba su yi aiki yadda ya kamata ba, sannan kuri’in da aka kada sun fi yawan mutanen da aka tantance a zaben.
Kotun ta ce karar da PD da dan takarata suka daukaka ba ta da amfani saboda sun kasa ayyana rumfunan zabe da jami’an da suka yi aiki a rumfunan da abubuwan da suke zargi sun faru.
Tun da farko Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Gwamnan Jihar Kogi wadda ta yi zamanta a Abuja ta yi watsi da zargin dan takarar. Daga baya a watan Agusta Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin.
Ana dakon hukuncin da alkalan kotun za su yanken game da karar da ‘yar takarar Jam’iyyar SPD a zaben, Natasha Akpoti, ta daukaka, na kalubalantar sakamakon zaben.
Karin bayani na tafe…