Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya gabatar da kasafin 2022 na Naira biliyan 154.61 ga Majalisar Dokokin Jihar.
Da yake bayanin kasafin a gaban majalisar, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, ya ce kasafin ya kunshi Naira biliyan N69.117 na manyan ayyuka (kashi 44.7 cikin 100), sai biliyan 85.393 (kashi 55.3 cikin 100) na ayyukan yau da kullum.
A cewarsa, za a kashe kudaden ne bisa hasashen samun kudaden shiga Naira biliyan 73.626 da gwamnatin jihar za ta samu a shekarar 2022.
Bangarorin da gwamnatin jihar take sa ran samun kudaden shigar a shekarar su ne harajin cikin gida Naira biliyan 13.225.
Suaran su ne harajin sayayyan kayayyaki (VAT) Naira biliyan 18, sai kuma kudaden da ake ware wa bangarorin gwamnati Naira biliyan 36.
A jawabinsa, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Gombe, Abubakar Mohammad Luggerewo, ya tabbatar wa gwamnan cewa za su duba kundin kasafin kudin domin kammala aikin a kansa da wuri ya zama doka.
Luggerewo, ya kuma yaba wa gwamnan kan yadda ya gudanar da ayyukan raya kasa a fadin jihar, musamman a bangaren ilimi, samar da ruwan sha da kiwon lafiya, inda aka kwaskware tare da daga darajar wasu manyan asibitoci a sassan jihar.