✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Haƙar Man Kolmani: Gwamnan Gombe ya gana da Tinubu

Gwamnan ya ce ya tattauna da Tinubu kan halin tsadar rayuwa da ake ciki a faɗin ƙasar nan.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, ya gana da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu kan tsayawar aikin haƙar man fetur a yankin Kolmani.

Gwamnan ya ce ganawar tasu na da muhimmanci, domin sun tattauna abubuawa da dama.

A cewarsa shugaba Tinubu na kan turbar wajen ganin ya cika alƙawura da haƙƙoƙin da aka ɗora masa.

A sakon da mai magana da yawun gwamnan, Isma’ila Uba Misilli, ya fitar, ya nuna damuwar kan yadda aikin haƙar mai na Kolmani ya tsaya kusan tsawon shekara biyu tun bayan ƙaddamar da shi.

Gwaman ya ce abin takaici ne yadda haƙar man ya tsaya, wanda wannan shi ne dalilin da ya sa ya gana da shugaban ƙasa.

Kazalika, ya ce sun tattauna kan batun tsadar rayuwa wanda hakan ta sa ya ɓullo da shiirn noman rogo a faɗin jihar mai tsawon kadada 500.

Sannan ya ɗauki ɗamarar raba taki da ya kai tan 2000 a farashi mai sauƙi ga manoma wanda tuni aka fara sayar da shi kan Naira 25,000 maimakon Naira 43,000 da ’yan kasuwa ke sayarwa.