✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Filato ya dakatar da ma’aikatan da Lalong ya dauka

Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya dakatar da duk ma’aikatan da tsohon gwamnan jihar, Simon Lalong ya dauka, daga shekara ta 2022 zuwa karshen wa’adinsa

Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya dakatar da duk ma’aikatan da tsohon gwamnan jihar, Simon Lalong ya dauka, daga shekara ta 2022 zuwa karshen wa’adinsa.

Wata sanarwa mai dauke da sanya hanun daraktan watsa labaran gwamnan, Gyang Bere ta ce an dakatar da ma’aikata ne saboda an saba ka’ida wajen daukar su.

Ta kara da cewa ma’aikatan da dakatarwar ta shafa suna wadanda aka dauka daga watan Oktobar 2022, zuwa karewar wa’adin Lalong.

“Dukkan ma’aikatan da lokacin ritayarsu ya cika amma ba su bar ofisoshinsu ba, saboda an kara masu lokaci, ko kuma ma’aikatan da aka dauka bisa kwantaragi su gaggauta mika kayan gwamnati da ke hanunsu.”