✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnan Bauchi ya ba zakarun musabaka ta kasa kyautar miliyan uku-uku

Gwamnan ya kuma yi alkawarin daukar nauyin karatun zakarun gasar har zuwa kammala karatunsu

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad, ya bayar da kyautar Naira miliyan uku-uku ga zakarun musabakar Alkur’ani ta kasa da aka gudanar a Jihar.

Ya bayar da kyautar ne ga wadanda suka yi na daya a izu 60 daga bangaren maza da mata a lokacin da ake bikin rufe gasar karo na 36 a jihar Bauchi.

Dan Jihar Borno, Baba Sanyinna Goni Muktar ne ya zama zakaran gasar a bangaren maza, inda ’yar jihar Zamfara, Haulatu Aminu Ishaq ta lashe kyautar daga bangaren mata.

Har ila yau, Gwamnan ya kuma yi alkawarin daukar nauyin karatun zakarun gasar har zuwa kammala karatunsu.

Wannan ne dai karo na 36 da ake gudanar da gasar da Jami’ar Usman Danfodio da ke Sokoto ke jagoranta.