Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya sanya dokar hana fita a Kananan Hukumomin Jihar bakwai don dakile ta’addancin kungiyar ’yan awaren Biyafara ta IPOB.
Kananan Hukumomin da dokar ta shafa sune Aguata da Ihiala da Ekwusigo da Nnewi ta Arewa da Nnewi ta Kudu da Orumba ta Arewa da kuma Orumba ta Kudu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wani jawabin da ya yi wa al’ummar Jihar da yammacin Laraba.
Ya ce dokar, wacce za ta fara aiki daga ranar Alhamis mai zuwa za ta ci gaba har sai zaman lafiya ya dawo yankunan.
A cewar Farfesa Soludo, “Daga ranar Alhamis, 26 ga watan Mayun 2022, mun sanya dokar hana fita daga karfe 6:00 na yamma har zuwa 6:00 na safe ga babura masu kafa biyu da masu kafa uku da ma motocin haya.
“Dokar za ta yi aiki ne a Kananan Hukumomin Aguata da Ihiala da Ekwusigo da Nnewi ta Arewa da Nnewi ta Kudu da Orumba ta Arewa da kuma Orumba ta Kudu, har sai abin da hali ya yi.
“Kazalika, mun hana zirga-zirgar babura masu kafa biyu da masu kafa uku da motocin bas-bas a wadannan Kananan Hukumomin a duk ranakun Litinin, har sai an daina dokar zaman gida,” inji shi.
Daukar matakin na zuwa ne kwana biyu bayan ’yan kungiyar sun kashe wata mai juna-biyu ’yar Arewacin Najeriya tare da ’ya’yanta su hudu, lamarin da ya jawo suka da Allah-wadai daga mutane da dama.
Ko a makon da ya gabata ma, ’yan ta’addan sun fille kan dan Majalisar Jihar ta Anambra da ke wakiltar mazabar da Gwamna Soludo ya fito.