✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Anambra na farko, Chukwuemeka Ezeife ya rasu

Gwamnan Jihar Anambra na farko kuma jigo ne a kungilar kabilar Igbo ta Ohaneze Ndigbo Dokta Chukwuemeka Ezeife ya rasu

Gwamnan Jihar Anambra na farko, Dokta Chukwuemeka Ezeife ya riga mu gidan gaskiya.

Dokta Chukwuemeka Ezeife, wanda jigo ne a kungilar kabilar Igbo ta Ohaneze Ndigbo, ta rasu ne a sakamakon rashin lafiya a daren Alhamis.

Ya rasu ne a Babban Asibitin Tarayya da ke Abuja, kamar yadda Cif Rob Nawkairea Ezeife ya sanar a madadin iyalan mamacin.

“Muna sanar da rasuwar danmu, Chukwuemeka Ezeife, CON, tsohon Babban Sakatare kuma Kwamnan Jihar Anambra na farko”

Chukwuemeka Ezeife tsohon mashawarcin shugaban kasa ne, kuma tsohon mai neman takarar shugaban kasa.

“Nan gaba za mu sanar da tsare-tsaren jana’izar,” in ji sanarwar rasuwar.