✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnan Abia ya ba ‘yan kwangilar Gwamnatin Tarayya wa’adi

Gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu ya ba ‘yan kwangilar da Gwamnatin Tarayya ta ba aikin manyan titinan Enugu-Port Harcourt da Aba-Ikot Ekpene wa’adin 20 ga…

Gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu ya ba ‘yan kwangilar da Gwamnatin Tarayya ta ba aikin manyan titinan Enugu-Port Harcourt da Aba-Ikot Ekpene wa’adin 20 ga watan Nuwamba, 2020 ko kuma su tsaya gwamnatin jihar ta ci gaba da nata bangaren.

Ikpeazu ya bayar da wa’adin ne a wata ganawa da ‘yan jarida a gidan gwamnatin jihar ranar Asabar.

Ya bayyana muhimmancin hanyoyin, musanman ta fuskar hada-hadar kasuwanci ga jama’ar jihar.

Gwamnan ya ce hanyoyi masu kyau jigo ne ga bunkasa kasuwanci da tattalin arziki, kuma hakan na daga cikin kudurin gwamnatinsa.

Ya ba wa Kwamishinan Kudi da Ayyuka umarnin tabbatar da biyan dukkannin ‘yan kwangilar da ke gudanar da ayyukan hanyoyi a fadin jihar.

Ikpeazu ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci sakaci ko rashin ingancin ayyuka daga ‘yan kwangila ba.

Ya ce gwamnatin jihar ba ta karbi ko sisi daga Gwamnatin Tarayya na ayyukan hanyoyi Gwamnatin Tarayya da jihar ta kammala ginawa ba.