Gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu ya ba ‘yan kwangilar da Gwamnatin Tarayya ta ba aikin manyan titinan Enugu-Port Harcourt da Aba-Ikot Ekpene wa’adin 20 ga watan Nuwamba, 2020 ko kuma su tsaya gwamnatin jihar ta ci gaba da nata bangaren.
Ikpeazu ya bayar da wa’adin ne a wata ganawa da ‘yan jarida a gidan gwamnatin jihar ranar Asabar.
- Harbin Lekki: Sojoji sun kawo bidiyon abin da ya faru
- An kubutar da matashi baya awa bakwai a cikin kwata
- Mutum 18 sun mutu a nutsewar kwalekwale a Bauchi
Ya bayyana muhimmancin hanyoyin, musanman ta fuskar hada-hadar kasuwanci ga jama’ar jihar.
Gwamnan ya ce hanyoyi masu kyau jigo ne ga bunkasa kasuwanci da tattalin arziki, kuma hakan na daga cikin kudurin gwamnatinsa.
Ya ba wa Kwamishinan Kudi da Ayyuka umarnin tabbatar da biyan dukkannin ‘yan kwangilar da ke gudanar da ayyukan hanyoyi a fadin jihar.
Ikpeazu ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci sakaci ko rashin ingancin ayyuka daga ‘yan kwangila ba.
Ya ce gwamnatin jihar ba ta karbi ko sisi daga Gwamnatin Tarayya na ayyukan hanyoyi Gwamnatin Tarayya da jihar ta kammala ginawa ba.