✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Zulum ya gabatar da kasafin kudin badi na Naira biliyan 134.5

Bangaren Ilimi ya samu kaso mai tsoka bayan da  Gwamna Babagana Umara Zulum ya gabatar da kasafin kudin Jihar Borno  da ya kai Naira biliyan…

Bangaren Ilimi ya samu kaso mai tsoka bayan da  Gwamna Babagana Umara Zulum ya gabatar da kasafin kudin Jihar Borno  da ya kai Naira biliyan 134.5 a kasafin badi

Gwamna Babagana Umara Zulum ya ce bangaren ilimi zai kwashi kaso mai tsoka ganin halin da harkar ilimi ta samu kanta a ciki a Jihar Borno a dalilin fitinar Boko Haram. Gwamna ya bayyana haka ne,  lokacin da yake gabatar da kasafin kudin badi a gaban Majalisar Dokokin Jihar a Maiduguri a ranar Litinin da ta gabata.

Farfesa Zulum ya ce duk wasu ayyuka da suka shafi harkar ilimi, za su samu kyakkyawar kula a kasafin kudin, inda aka ware wa sashin ilimin Naira biliyan 23 a  kasafin mai taken ‘Inganta Jihar Borno.’

Gwamna Zulum ya ce Naira biliyan 67.5 wato kashi 53 cikin 100 na kasafin zai tafi ga ayyukan yau da kullum, sai Naira biliyan 69.9 aka ware don manyan ayyuka.

Ana sa ran samun akasarin kudaden daga Asusun Tarayya.

Gwamnan ya bayyana ware Naira biliyan 23 ga fannin ilimi, inda daga ciki aka ware Naira biliyan 19.1 domin manyan makarantu, da bada fifiko ga Jami’ar Jihar Borno (BOSU), baya ga haka akwai niyyar ta gina makarantun firamare na zamani guda 7 da kuma sakandare da manyan makarantu.

Haka an ware wa Ma’aikatar Kudi, Naira biliyan 19.1 wacce za ta kasance gidauniya wajen gudanar da ayyukan gwamnati, sai Naira biliyan 11.6 ga harkar kiwon lafiya, Naira biliyan 9.2 domin sake gina garuruwan da ’yan Boko Haram suka lalata. Sai Naira biliyan 7 don gina hanyoyi da sauran ayyukan da suka jibanci haka. Bayan haka an kuma ware Naira biliyan 5.3 don ayyukan majalisa, sai Naira biliyan 4.4 wajen gina rukunin gidaje, Naira biliyan 4 aka ware wa sashin aikin gini.

Gwamna Babagana Zulum ya ce “A kasafin badi za mu gina makarantu na musamman guda biyu a Wuyo da Chibok da kuma makarantun koyon sana’o’i guda a garin Mbalala da Unguwar Bulaburin a birnin Maiduguri. Haka za mu gina manyan makarantun gaba da sakandare a fannin addinin Musulunci guda uku a garuruwan Dikwa da Monguno da  Biu.” inji Gwamna Zulum.

Har Ila yau Zulum ya bayyana cewa Gwamnatinsa za ta farfado da kuma buDe makarantun sakandire dake garuruwan Monguno, Damasak,Gajiram, Gubio da Dikwa, Ngala, Konduga, Bama da Gwoza wadanda a da duk sun kasance a rufe a dalilin ta’addacin Boko Haram.

Farfesa Zulum ya kara da cewa  a kasafin akwai tsari na gina ajujuwa 72 a fadin jihar gaba daya, baya ga sake gina wadanda suka lalace a dukkan kananan hukumomi 27 ta wajen gina ajujuwa biyu-biyu.

Ya kuma bayyana cewa za a dauki malamai 1000 domin cike gibi, hada da sayo kujeru da tebura, da saura kayan aiki, Wanda za a samar ga dukkan makarantun da aka sake gyara su,, Gwamna Zulum ya bada tabbacin cewar gwamnatinsa za ta ci gaba da tsarin nan na ciyar da dalibai a dukkan fadin jihar ta Borno.

Zulum ya sake jaddada bada muhimmancin a fannin ilimi a wannan kasafin, ya ce akalla makarantun firamare 20 da na gaba da firamare za a farfado da su ta hanyar manyan ayyuka a sassa dabam dabam a fadin jihar.

Gwamna ya ce akwai sabbin makarantun na zamani guda 3, Wanda zai kunshi dalibai 1,200, Wanda tuni an gina hada da samar musu da kayayyakin aiki na zamani, Wanda tuni aka bude su, a farkon watanni shida na wannan gwamnati.