✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna ya raba wa limaman addinai da suka yi masa addu’a Naira miliyan 30

Limamai a Jihar Kuros Riba sun gode wa Farfesa sanata Ben Ayade, Gwamnan Jihar Kuros Riba bisa alkawarin da ya yi musu wata bakwai ke…

Limamai a Jihar Kuros Riba sun gode wa Farfesa sanata Ben Ayade, Gwamnan Jihar Kuros Riba bisa alkawarin da ya yi musu wata bakwai ke  nan, bayan da ya samu nasara a kotun daukaka kararakin zabe a watannin baya ne  ya yi wa  kungiyar addinan Kirista da Musulmi alkawarin ba su Naira milyan 30, saboda addu,oi da ya  ce sun dage yi masa lokacin da suka yi shari’a zabe.

A makon jiya ne gwmnan ya kirawo shugabannin kungiyar limamai da alarammomi ya ba su kyautar Naira milyan bakwai domin raba wa daukacin limamai da ke jihar. Da yake zantawa da Aminiya a Kalaba Shugaban kungiyar Limamai da Alarammomi na Jihar Kuros Riba Manjo Kabiru Sa’ad Yakubu ya gode wa gwamnan bisa cika alkawarin da ya yi.

“Gaskiya mun yi murna, mun yi farin ciki matuka da gwamnan ya cika mana alkawari ya ba mu Naira milyan bakwai,”inji Yakubu

A cewar  shugaban limaman: “An ba kowane limami Naira dubu 100. Kuma hatta sarakunan mu na gargajiya ma an ba su Naira milyan daya da dubu 200, sai abokan aiki na gefe suma an nema musu wani abu.”.

Manjo Sa’ad Yakubu babban Limamin Barakin Soja Birged ta 13 da ke Kalaba, wanda shi ne shugaban kungiyar ya jawo hankalin ragowar limaman masallatai da suka nuna turjiyar kin shiga kungiyar da cewa ba kungiya ce mai adawa da akida ko ra’ayin addini mutum ba, “a,a domin a yi wa Musulunci aiki da kuma Musulmi.”

karshe ya bayyana cewa sun ajiye wa sakatariyar kungiyar wani abu, domin ci gaba da gudanar da ayyukanta. 

“Maimakon mu rika zuwa bara wurin mutane ya sa muka ware wa sakatariya wani abu,” inji shi.