Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo, ya haramta amfani da karamin siket a matsayin kayan makaranta ga dalibai mata a ilahirin makarantun da ke jihar.
Kwamishiniyar Ilmi ta jihar, Ngozi Chuma-Udeh, wacce ta sanar da hakan ranar Lahadi, ta ce umarnin ya zama file yayin da makarantun jihar ke kokarin komawa sabon zangon karatu a ranar Litinin.
- Mutum 19 sun kone kurmus a hatsarin mota a Abuja
- Amotekun za ta fara amfani da kudan-zuma da macizai wajen yaki da ta’ddanci a Oyo
Ta ce tuni aka aike da umarnin ga Sakatarorin Ilimin jihar, kuma zai shafi dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu da ke jihar.
Kwamishiniyar, wacce ta koka da sabon yayin dinka karamin siket din ga dalibai mata, ta ce hakan bai dace da tarbiyyarsu ba, la’akari da shekarunsu.
“Ya kamata daliba ta kasance tsaf, mai tarbiyya kuma mai sanin ya-kamata ba wai ta yi shigar banza ba a makaranta.
“Kayan da aka amince a yi amfani da su a matsayin na makaranta su ne wanda suka kai idon-sahu, amma ba iya gwiwa ba. Mun lura hakan na neman zama wani yayi sabon a makarantunmu,” inji ta.
Daga nan sai Kwamishiniyar ta hori Sakatarorin Ilimin da su tabbatar makarantu sun kiyaye dokar da kuma yin amfani da ita. (NAN)