✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Seyi Makinde ya kamu da Coronavirus

Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde, ya bayyana cewa gwajin da aka yi masa na cutar Coronavirus ya nuna cewa yana dauke da cutar. Seyi Makinde,…

Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde, ya bayyana cewa gwajin da aka yi masa na cutar Coronavirus ya nuna cewa yana dauke da cutar.

Seyi Makinde, ya shaida hakan ne a shafinsa na Twitter @seyiamakinde, da yammacin yau Litinin inda ya bai wa tsohon babban Daraktan sashin lafiya na Asibitin koyarwa na jami’ar Ibadan Farfesa Temitope Alonge, jan ragamar tawagar da ke kula da yaduwar cutar Coronavirus a jihar.

Gwamnan jihar Oyo, ya yi kira ga al’umar jihar da su yi biyayya ga tawagar da ke kula da cutar kana su yi amfani da shawarwarin da za su basu.

“Ku zauna a gida, ku kula da kan ku,” in ji shi.

Sanarwar kamuwar gwamnan jihar Oyo tazo ne cikin sa’o’i kadan bayan da babban jami’in na asibitin koyarwa na jami’ar Ibadan Farfesa Jesse Abiodun Otegbayo ya kamu da cutar a jihar Oyo.