✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Masari ya bukaci sojoji kada su raga wa ’yan bidigar da suka ki sulhu

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya yi kira ga sojoji da kada su ragawa duk wani dan bindigar da ya karya alkawalin sasancin da…

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya yi kira ga sojoji da kada su ragawa duk wani dan bindigar da ya karya alkawalin sasancin da aka yi da su domin samun zaman lafiya. Gwamna Masari ya yi wannan kira ne a ranar Juma’ar da ta gabata a lokacin da ya karbi bakuncin wasu manyan shugabannin Hedkwatar sojojin Najeriya da ke Abuja a karkashin jagorancin babban jami’in horarwa na rundunar Janar Leo Irabor.

Gwamnan ya ce, “Ina jinjina tare da yabawa sojojin bisa irin sakamako mai kyau da ake samu a lokuttan da suke aiwatar da ayyukansu a fadin kasa baki daya musamman akan abin da ya shafi samar da zaman fiye da yadda muke tunani.”

Gwamna Masari ya ce duk dan bindigar da suka yi watsi da shiri tare da yarjejeniyar samar da zaman lafiyar da aka cimma, sojojin su dauki duk matakin da ya kamata akansu saboda sun nuna rashin mutunci da kuma kin son zaman lafiya.

Gwamnan ya bayyana cewa ana bukatar a sake bullo da wasu hanyoyin don shawo kan matsalar tsaron da ake ciki, sannan ya yi kira ga jami’an ’yan sanda da su yi tunani tare da kirkiro hanyoyin da za su shawo kan matsalar, wanda hakan zai kara inganta ayyukansu.

Da yake mayar da jawabi, Janar Leo Irabor ya yabawa Gwamna Masari akan irin hadin kai da kuma gudunmuwar da yake ba jami’an sojojin da sauran takwarorinsu. Ya ce Gwamnan mutun ne wanda yake ba harkar tsaro muhimmanci sosai, wanda hakan ya sa jihar take cikin jihohin da suke da tsaro a kasar. Sannan ya ce zasu kara yin damara don kalubalantar duk wani wanda zai kawowa kasa rashin zaman lafiya.