✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Masari bai sa an tsare ni ba – Ricardo

Wani matashin dan siyasa mai suna Babangida Muhammed da ya fito daga mazabar Wawala-Kaza a karamar Hukumar kankara a Jihar Katsina ya musanta jita-jitar da…

Wani matashin dan siyasa mai suna Babangida Muhammed da ya fito daga mazabar Wawala-Kaza a karamar Hukumar kankara a Jihar Katsina ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya sa an tsare shi.

Babangida Muhammed wanda aka fi sani da Babangida Ricardo ya bayyana haka ne lokacin da ya kawo ziyara ofishin Aminiya da ke Abuja, inda ya ce, “Ya kamata wadnsu daga cikin shugabannin Jam’iyyar APC a mazabata ta Wawala-Kaza su ji tsoron Allah, su daina sanya sunan  Gwamna Masari a cikin abin da babu ruwansa. Gwamnan Masari mutum ne kamili, don haka ba yadda za a yi ya sanya a kama ni a tsare ni.”

“Mun samu wata matsalar siyasa da wani abokin siyasa daga karamar Hukumar kafur inda Gwamnan ya fito, inda lamarin ya kai har kotu. Amma ko kadan Gwamna bai da masaniya. Don haka cewa wai Gwamnan ne ya sa aka tsare ni, batanci ne gare shi domin ya wuce haka kuma ba halinsa ba ne,” inji shi.

Babangida ya kara da cewa, “Shi kansa wanda muka samu matsalar da shi tuni mun yi sulhu, kuma yanzu haka ya zama uban gidana a siyasa. Amma abin mamaki shi ne yadda wadansu suke amfani da abin wajen yarfe da batanci gare ni, da kuma shi kansa mai girma Gwamnan Jihar Katsina.

Kuma kasancewar idan aka kirga mutum 10 a karamar Hukumar kankara da suka yi kokari wajen tabbatar da an zabi Gwamna Masari da Shugaba Buhari, dole da ni a ciki. Shi kansa Gwamna ya san da haka. Kuma ko zaben 2019 ina nan a kan bakana, da yardar Allah sai Gwamna Aminu Bello Masari da Shugaba Buhari sun koma mulki, domin su ci gaba da ayyukan alherin da suka fara.”