Gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalong ya yi alkawarin ci gaba da tabbatar da rashin nuna banbanci da san zuciya ga duk ’yan jihar ta fannin qabila ko addini ko kuma banbancin siyasa. Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan rantsar da shi da aka yi jiya Laraba a matsayin Gwamnan jihar karo na biyu.
Gwamna Lalong, ya ce jihar Filato ta kasance jiha ce da take da kabilu da dama, sannan ya ce a wannan karon za a rarraba ayyukan jihar ga inda aka fi bukata. Hakan zai tabbatar da yin adalci ga jama’ar da suka kada kuri’ar su don samun ci gaba a jihar.