✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Gaidam ya nemi a guji siyasar a-mutu-ko-a-yi-rai

Gwamna Ibrahim Gaidam na Jihar Yobe ya hori al’ummar jahar musamman ’yan siyasa da su guji tsarin siyasar nan na ko a-mutu-ko-a-yi-rai, wadda ya ce…

Gwamna Ibrahim Geidam na Jihar YobeGwamna Ibrahim Gaidam na Jihar Yobe ya hori al’ummar jahar musamman ’yan siyasa da su guji tsarin siyasar nan na ko a-mutu-ko-a-yi-rai, wadda ya ce hakan ba zai taimaka ba ga ciyar da mulkin dimokuradiyya gaba a cikin al’umma da kuma uwa-uba harkokin da suka shafi ci gaba da samar da yanayin tsaro mai inaganci.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin mataimakinsa Injiniya Abubakar Ali a cikin sakonsa na Sallah yayin da ya karbi wata tawagar ’yan siyasa daga kananan hukumomin Potiskum da Fika da Nangere da Fune a karkashin jagorancin Mista Hassan Jonga a ziyarar da suka kai gidan gwamnati a Damaturu.
Gwamna Gaidam ya ci gaba da cewar ya yi imanin ita siyasa  ba wata aba ba ce illa hanyar ciyar da al’umma gaba, amma ba hanya ce ta ko a mutu ko a yi rai ba, kamar yadda wasu ’yan siyasar ke da akidar hakan, lamarin da babban koma baya ne ga hadin kan al’umma.
Ya kirayi ’yan siyasa su rika daukar kansu a matsayin jagororin hada kan jama’a, ba rarraba kansu ba, don a samu sakamako mai kyau, wanda zai ciyar da jihar da ma kasa gaba, musamman a wannan yanayin da ake ciki na tabarbarewar harkokin tsaro.
Ya jaddada bukatar da ke akwai ta nuna halin hakuri da juriya, wadanda su ne hanyoyin bi don kawar da bambance-bambancen da ke tsakanin al’umma, ta yadda za a samu ci gaba mai armashi.
Tun farko a nasa jawabin, jagoran tawagar, wadda ta fito daga shiyyar kudancin Yobe, Mista Hassan Jonga ya bayyana sun zo gidan gwamnatin ne don taya gwamnan da mataimakinsa murnar kammala azumin watan Ramadan.
Ya ce sun yi na’am da gwamnatin Ibrahim Gaidam, “Wadda ke kula da hakkokin talakawanta, lamarin da shi ne ma ya sa ya koma jam’iyyar ANPP, ya bar tsohuwar jam’iyyasa ta PDP.
Don haka abin a yaba ne irin yadda gwamnmatin ke kokarin gudanar da muhimman ayyukan raya kasa, duk da irin kalubalen da ke gabanta kan tabarbarewar harkokin tsaro da jihar ta yi fama da shi na tsawon sama da shekaru biyu”. Inji shi.