✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna dankwambo ya ba kungiyar RTEAN rancen motoci da Keke NAPEP

kungiyar masu motocin haya ta Najeriya (Road Transport Employers Association of Nigeria -RTEAN), reshen Jihar Gombe, ta amfana da tsarin da Gwamna Ibrahim Hassan dankwambo…

kungiyar masu motocin haya ta Najeriya (Road Transport Employers Association of Nigeria -RTEAN), reshen Jihar Gombe, ta amfana da tsarin da Gwamna Ibrahim Hassan dankwambo ya bullo da shi na bayar da motoci da Keke NAPEP da ake wa lakabin Tasin Talba a jihar.
Shugaban kungiyar, Alhaji Kabiru Magaji ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce kungiyar ta amfana da motoci hamsin da Kekuna hamsin, kowace mota tana da kimar Naira miliyan biyu da dubu dari shida, kuma kowane keke yana kan Naira dubu dari biyar, wadanda kudinsu ya kai Naira miliyan dari da hamsin a matsayin bashi don inganta sana’arsu ta sufuri.
Shugaban ya yi na’am da tallafin da aka ba su, wanda mutum dari biyu suke cin moriyarsa domin a halin da ake ciki kowace mota tana da direbobi uku, haka ma shi Keke NAPEP din.
Alhaji Kabiru ya ce, “Mun ji dadin wannan al’amari, musamman ganin yadda kungiyarmu ta kara samar wa matasa aikin yi, tun ma dai ba in aka yi la’akari da halin rayuwa da ake ciki yanzu”.  
Alhaji Kabiru ya ce ba su wadannan ababen hawa don inganta sana’arsu ya fi musu mukamin siyasa na S.A. ko P.A.,  saboda, a cewarsa, “A inganta maka sana’arka, a taimake ka a kai, ya fi a ba ka mukamin siyasa, wanda idan siyasar ta wuce, shi ke nan an bar ka da yawon maula”.
Ya yi bayanin cewa hukumar kare hadurra ta kasa (FRSC) tare da ta jami’an kula da ababen hawa sun hadu sun bai wa direbobinsu horo kan yadda za su kula da ababen hawan sosai kuma su  kiyaye faruwar hadurra a lokacin da suke tuki.
Daga nan kuma ya jinjina wa Gwamna dankwambo kan yadda yake gina babbar tashar mota ta zamani a jihar.