✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Ajimobi ya sha alwashin gano makasan dan majalisa

Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, ya ce da taimakon Allah za a gano tare da kama ko su wane ne ke da hannu wajen…

Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, ya ce da taimakon Allah za a gano tare da kama ko su wane ne ke da hannu wajen kisan gillar da aka yi wa dan majalisar dokoki na jihar Mista Gideon Aremu, wanda wasu ’yan bindiga suka kashe a cikin daren Juma’ar da ta gabata.
Gwamnan wanda tuni ya bayar da umarni ga rundunonin tsaro na ’yan sanda da soja da su hanzarta daukar matakin yin bincike domin gano wadanda suka yi kisan gillar, ya roki Allah Ya tona asirinsu cikin kankanen lokaci domin kama su da hukunta su.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci wasu kusoshin gwamnati zuwa gaisuwar ta’aziya da jajanta wa iyalan marigayin, a gidansa da ke Alakia, Ibadan. Ya ce: “Nan da dan lokaci kankane asirinsu zai tonu idan Allah Ya yarda.” Ya nuna matukar bakin cikinsa da wannan danyen aiki da ’yan bindigar suka aikanta, inda suka bi sawun dan majalisar har cikin gidansa suka bindige shi. Ya ce, wannan alama ce ta dawowar tashe-tashen hankula da gwamnatinsa ta yi maganinsu a cikin shekarun da ta yi a kan gado. Ya ce: “Idan kun tuna a cikin shekara ta 2011 ne muka tabbatar da dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali, wanda aka daina samun labarin kashe-kashen mutane da suka shafi siyasa da fashi da makami da makamantansu a jihar. Kisan gillar da aka yi wa dan majalisa Gideon Aremu, alama ce ta farko na sake dawo da irin wannan danyen aiki bayan shekaru masu yawa da aka yi adabo da su.”  Inji Gwamnan.
Da yake jajanta wa matar marigayin, Uwargida Bukola Aremu da ’ya’yansu, Gwamnan ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta taimaka wajen daukar dawainiyar al’amuran da suka shafi rayuwarsu baki daya. Iyalan marigayin da hadin gwiwar gwamnati sun kammala shirin yi wa marigayin jana’iza da binne shi a mahaifarsa, wato garin Igboho da ke karamar Hukumar Oorelope.
An tabbbatar da cewa ’yan bindigan da suka kashe shi, su uku ne da suke kan babur da suka cire wayoyin salula guda biyu daga cikin aljihun dan majalisar suka yi awon gaba da su ba tare da daukar motarsa ko kudin da ke cikin aljihunsa a lokacin ta’addacin nasu ba. Marigayi Gideon Aremu, mai shekaru 42, yana wakiltar mazabar Oorelope a majalisar dokoki ta Jihar Oyo, a karkashin inuwar jam’iyar Labour ne.
Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Oyo, CP Leye Oyebade, wanda shi ma ya kai irin wannan ziyara zuwa gidan marigayin ya bayar da umarnin yin bincike domin gano dalilin kisan. Ya tabbatar da cewa ’yan sanda za su gayyaci wasu mutane da bai fadi sunayensu ba da za a yi wa tambayoyi dangane da mutuwar dan majalisar.