Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu ya rufe ƙofar Gidan Gwamnati ranar Alhamis saboda taron ma’aikatan da suka makara.
Gwamnan ya tuƙa kansa zuwa ofishinsa da ƙarfe 8:30 na safe amma ya tarar mafi yawan ma’aikata sun makara.
Sai masu shara ya tarar da wata nas ɗaya a asibitin dake cikin Gidan Gwamnati.
Musulman Sokoto za su kaurace wa taron kungiyar lauyoyi
Gwamnan Sokoto ya yi ganawar sirri da Obasanjo
Don haka ya sa masu gadi suka rufe ƙofa kuma ya hana kowa shiga har sai bayan ƙarfe 1:00 na rana.
Da yake tattaunawa da wakilin Aminiya, gwamnan ya ce “wanann ba maganar wasa ba ce.
“Cikin mako uku da hawana na biyu albashin watanni biyu.
“Shi ya sa na tuƙo kaina da na ga direban ya makara.
“Amma ba zan gaya maka matakin da zan ɗauka na gaba ba saboda kai ma ka makara.”
Gwaman ya kuma ce ya yi alƙawarin ba zai ci amanar al’ummar Sokoto kuma ba zai bari ma’aikata da jami’an gwamnati su ci amanarsu ba.
Ya ƙara da cewa, “Ko dai ka yi aiki ko ka dawo mana da kuɗinmu. Ba zaka karɓi kuɗinmu ka gaza cika aikinka ba.”