✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwajin soyayya

Wata rana wani malami yana zaune da jama’a ana ta hira, sai ya tambaye su cewa: “Anya kuwa kuna son matayenku, kuna nuna musu kauna…

Wata rana wani malami yana zaune da jama’a ana ta hira, sai ya tambaye su cewa: “Anya kuwa kuna son matayenku, kuna nuna musu kauna sosai?” Gaba daya suka amsa da cewa: “kwarai kuwa.” Malamin ya sake cewa: “Yaushe rabon da kowannenku ya furta wa matarsa cewa yana son ta?” To a nan ne suka fara ba da amsa. Wani ya ce kusan wata guda ke nan, wani ya ce fiye da shekara, wani ya ce ba zai iya tunawa ba, da sauransu.
Malam ya ce: “Kowa ya rubuta sakon: “Ina son ki” ta wayar salula ya aika wa matarsa, domin ganin wadanne irin amsoshi za su bayar?”
Cikin kankanin lokaci sai ga amsoshi sun fara zuwa daga wajen matayen kamar haka: 1-“Mhm! Da ke nan banda yanzu.” 2-“Maganar auren naka ta rushe ke nan?” 3-“Kana son na ba ka aron kudi ke nan?” 4-“A mafarki ke nan!” 5-“Allah Ya kama ka, bari ka dawo ka fada mini wadda ka aika wa wannan sakon.” 6-“Mhm! Me kake nufi? Wannan karon ba zan yarda ba.” 7-“Waye wannan?” 8-“Wata sabuwa!” 9-“Yau kuma?” 10-“Hmmn! Munafiki, wallahi ban hakura da abin da ka yi mini ba.”
11-“Kana so na din banza!” 12-“Na fada maka ka daina shaye-shaye!”
Daga Ahmed Garba Mohammed, 08028797883