✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gurbatacciyar Hodar Iblis ta kashe mutum 20 a Argentina

Likitoci sun ce mamatan sun wahala da bugun zuciya gabannin ajalinsu.

Hukumomin kasar Argentina sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 20 yayin da wasu 84 ke kwance a asibiti, bayan shakar hodar iblis da wani sinadarin guba.

Rahotonnin likitoci na farko na cewa mamatan sun wahala da bugun zuciya gabannin ajalinsu bayan da suka shaki hodar iblis.

Jami’ai sun ce suna nan suna aiki cikin gaggawa don gano sinadaran da aka hada a cikin hodar iblis mai hatsari wanda ya yi ajalin mutane masu yawa.

Muhukuntan sun kuma gargadi wadanda suka sayi sinadaran da hodar iblis din a cikin sa’o’i 24 da suka wuce da su yi watsi da shi.

Tuni dai aka kama wani dillalin hodar iblis mai suna Joaquín “El Paisa” Aquino dan kasar Paraguay wanda mahukunta ke zargi na da hadi da gurbatacciyar hodar.