✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Gurbata muhalli: Kamfanin Shell zai biya kauyukan Neja Delta diyyar €15m

Shekara 15 ke nan ana tafka shari'a kan batun

Bayan shafe shekara 15 ana tafka shari’a, kamfanin mai na Shell ya amince ya biya wasu manoma uku da kauyukansu da ke yankin Neja Delta diyyar Yuro miliyan 15 saboda gurbata musu muhalli.

Manoman, tare da tallafin kungiyar Friends of the Earth (FoE) da ke kasar Netherlands da wasu lauyoyinsu biyu ’yan Najeriya ne dai suka maka kamfanin a gaban wata kotu da ke birnin Hague na Netherlands din tun a shekarar 2007.

Kauyukan da hukuncin ya shafa sun hada da Goi da Oruma da kuma Ikot Ada Udo.

Kotun dai a shekarar 2021 ta umarci kamfanin da ya biya diyyar saboda gurbata kasarsu da ya yi a tsakanin shekarun 2004 zuwa 2007.

Kauyen Goi dai yana Jihar Ribas, Oruma kuma a Bayelsa, yayin da Ikot Ada Udo yake Jihar Akwa Ibom.

A cikin wata sanarwar da ya fitar ranar Juma’a, Kakakin kungiyar FoEN a Najeriya, Philip Jakpor, ya bayyana nasarar a kotun a matsayin mai cike da tarihi.

Kakakin ya kuma ce kamfanin ya amince ya kafa na’urorin hana zubar mai don kiyaye gurbata muhallin a nan gaba.

Shi na da yake tsokaci kan hukuncin, daya daga cikin lauyoyin masu kara kuma Babban Daraktan FoEN, mai suna Williams, ya ce, jajircewar manoman da tsayawarsu kai da fata alama ce ta yadda sauran al’ummomin yankin ya kamata su zama wajen yaki da gurbacewar muhallansu. (NAN)