✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gumi ya caccaki ’yan siyasa kan barnar kudi a auren dan Buhari

’Yan siyasa sun kashe kudin jama’a a kan jiragen saman da ba na fasinja ba.

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi Allah wadai da yadda wasu masu ido da kwalli suka kece raini yayin halartar daurin auren Yusuf Buhari, dan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Sheikh Gumi ya yi tir da yadda manyan kasar nan da na ketare suka yi hayar jiragen da ba na fasinja domin halartar bikin da iyakacinsa da talaka sai dai ya ji labari ko kuma ya yi hange daga nesa.

A Juma’ar da ta gabata ce Yusuf Buhari ya auri Zarah Bayero, diyar Sarkin Bichi, Nasiru Bayero a wani kasaitaccen biki da aka gudanar a Fadar Sarkin Bichi da ke Jihar Kano.

Daurin auren ya samu halartar Shugaban Kasa Buhari, Mataimakinsa Yemi Osinbajo, Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan da Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar.

Akwai kuma masu ci da tsoffin gwamnoni, sarakunan gargajiya, da manyan mutane daga ciki da wajen kasar nan, ciki har da tsohon Shugaban Jamhuriyar Nijar Muhammadu Issofou.

Wani rahoto da sashen Hausa na Gidan Rediyon Faransa RFI ya wallafa, ya ce Shiekh Gumi ya caccaki ’yan siyasar ne yayin wani taron wa’azi a Masallacin Sultan Bello da ke garin Kaduna.

Yayin gabatar da wa’azin, Sheikh Gumi ya ba da misalin yadda Sahabin Manzon Allah (SAW) Umar bn Kattab ya taba daukar dinari 16 daga baitul mali a matsayin kudin zuwa aikin Hajji.

Amma bayan dawowar su, sai Umar (RA)ya koka cewa sun barnatar da dukiyar jama’a.

Gumi ya ce duba da misalin da ya bayar, babu hujjar da za ta sanya wasu mutane suna tsare a hannun masu garkuwa da su a cikin daji da birane, ga matsaloli iri iri, amma duk da haka ’yan siyasa sun kashe kudin jama’a a kan jiragen saman da ba na fasinja ba.

A cewar Malamin, wasu mutanen da ’yan fashi ke sacewa ba su ma taba samun naira miliyan daya a rayuwarsu ba, amma ’yan fashi za su bukaci naira miliyan 10 daga garesu.